✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amanawa: Garin kutare da ke neman agajin gwamnati

Babbar matsala da take addabar garin Amanawa ita ce rashin gonakin noma.

Amanawa sanannen gari ne na masu cutar kuturta da ke Karamar Hukumar Kalgo a Jihar Kebbi wanda aka kafa shi kimanin shekara 85 da suka gabata don killace mutanen da suke fama da cututtukan da suka shafi fata.

Garin mai nisan kilomita 7 daga Birnin Kebbi, Babban Birnin Jihar, a baya mazaunin Turawan Mishan ne locakin mulkin mallaka.

Amma bayan da Nijeriya ta samu ’yanci sai aka mayar da kauyen ya zama cibiyar ba da magani ga masu cutar kuturta da tarin fuka don rage wani bangare na Cibiyar Kula da Masu Cutar Kuturta da Tarin Fuka da ke Jihar Sakkwato.

Marigayi Sarkin Gwandu Alhaji Yahaya Ibn Halliru ne ya fara yunkurin kafa cibiyar, amma Sarkin Gwandu Haruna Rasheed ya tabbatar da ita bayan da ya kai masu cutar kuturta daga Sakkwato zuwa Amanawa.

A cewar Sarkin Kutaren Amanawa, Sarki Garba magabatansu da aka kawo sun gaji gidaje 80 da dakin shan magani da lambu da kuma babbar gona.

“A lokacin da Turawa suke zaune a nan garin muna zuwa ne kawai domin karbar magani amma bayan da Turawan suka tafi sai aka mallaka mana kauyen a matsayin mazauninmu na dindindin,” in ji Sarkin Kutaren.

Ya kara da cewa masu fama da larurar fata suna zaune ne a kauyen domin samun sauki wajen karbar magani.

Sai dai Aminiya da fahimci cewa duk da kusancin Amanawa da Birnin Kebbi, garin na fama da matsalolin da suke haifar da rashin ci gabansa.

Alal misali garin na fama da matsaloli a kusan duk abubuwan da suka shafi jin rayuwar dan Adam kamar bangaren lafiya da ilimi da noma da ba da tallafi da sauransu.

Asibitin garin na Amanawa wanda ke kula da masu larurar kuturta da sauran cututtukan fata ma na bukatar a yi masa kwaskwarima kuma a fadada shi.

Aminiya ta gano cewa makarantar firamare ta farko a kauyen an gina ta ce kimanin shakara 37 da suka wuce.

Bayan wasu shekaru sai ’yan Mishan suka canza wa makarantar mazauni kuma suka fadada ta bayan da suka gina rukunin azuzuwa biyu da ban-daki.

Amma bayan da ginin ya fara faduwa sai Gwamnatin Soji ta Kanar John Uba ta sake gina rukunin azuzuwa biyu da ban-daki domin ci gaba da koyar da dalibai.

Ita ma gwamnatin farar hula a karkashin tsohon Gwamnan Jihar, Sanata Atiku Abubakar Bagudu ta gina rukunin azuzuwa biyu da ban-daki a makarantar.

Duk da cewa har zuwa yanzu gine-ginen da ke makarantar nan, sai dai makarantar na fama da rashin malamai da kayan koyo da koyarwa ciki har da karancin littatttafai.

A lokacin da wakilin Aminiya ya ziyarci makarantar kimanin karfe 11 na safe ya tarar da malamai biyu ne kacal a zaune a ofishin shugaban makarantar, su kuma daliban da suka zo makaranta na cikin wani aji suna wasa.

Binciken da Aminiya ta gudanar ya nuna cewa cikin azuzuwa biyu da ke makarantar daya ne kacal ake amfani da shi, dayan kuma na cikin wani mummunan hali na saboda lalacewar da ya yi.

Haka Aminiya ta gano cewa baya ga Malam Muhammad Umar wanda a yanzu shi ne jami’i mai kula da asibitin garin babu wani dan garin da ya taba yin karatu zuwa gaba da sakandare.

Sai dai a yanzu haka kimanin ’yan garin 11 ne suke karatu a makarantar sakandare da ke garin Jega kuma iyayensu sun yi alkawarin ci gaba da daukar nauyinsu har zuwa makarantun gaba da sakandare domin karo ilmi.

Yadda Umar Muhmmad dan asalin garin ya kawo wa kauyen ci gaba An haifi Malam Umar Muhammad a garin Amanawa a 1974, kuma ya fara karatunsa na firamare a garin, amma daga bisani aka mai da shi firamaren garin Kalgo sakamakon faduwar ginin makarantar firamare ta Amanawa.

Bayan ya kammala firamare, Umar ya ci gaba da karatu a makarantar sakandaren Kalgo sannan ya wuce zuwa makarantar horar da malamai ta garin Argungu inda ya samu shaidar zama malamin makaranta (NCE).

Malam Umar ya fara koyarwa a garin Unguwar Aduwa tsawon mako daya kacal sai aka mayar da shi garin Uban Dawaki domin ci gaba da koyarwa inda nan kuma ya koyar har tsawon shekara daya da rabi.

A wannan gaba ce kuma Umar ya yanke shawarar canza akalarsa ta aiki domin biyan bukakarsa.

Don haka Malam Umar ya bar fannin koyarwa ya koma fannin kiwon lafiya bayan da ya koma makaranta ya samo horo a wannan fanni na lafiya.

Umar ya shaida wa Aminiya cewa, “Na koma fannin kiwon lafiya ne sakamakon wani abin takaici da wani shugaban asibitin kauyenmu ya yi wa iyayena a gabana.

“Wata rana ce a karshen mako lokacin da shi shugaban yake tattaunawa da iyayena a tsakiyar garin, sai daya daga cikin iyayena ya roke shi alfarma cewa ya yi amfani da matsayinsa ya roki gwamnati ta jawo mana wutar lantarki.

Budar bakin mutumin nan sai ya ce ai matukar shi ne shugaban asibitin to mu da wutar lantarki sai dai mu gani a titi.

Wannan maganar tasa ba shakka ta bakanta min rai ainun. “A takaice ma ban iya barci ba a wannan ranar, ina tunanin me ya kamata in yi in share wa iyayena hawayensu.

“To daga karshe sai na yanke shawarar canza fannin karatu zuwa fannin kiwon lafiya.

“Babban dalilina na yin haka shi ne domin ni ma in samu matsayi irin na shi wannan mutum da yaki yi wa iyayena alfarma domin in samu kusanci da gwamnati in taimaka wa iyayena da sauran al’ummar Annabi (SAW).

“Don haka a 1988 sai na koma karatu a Makarantar Koyar da Kimiyyar Kiwon Lafiya, (School of Health Technology) kuma na kammala a 2000.

“Da farko an kai ni garin Tungar Noma a matsayin baban jami’in asibitin garin na farko, domin sabon asibiti ne aka bude, inda na yi shekara daya da rabi a can.

“Daga bisani sai aka dawo da ni garinmu na Amanawa a matsayin babban jami’i mai kula da asibitin.

“Wannan shi ne matsayin da wancan mutumin da ya ki taimakon iyayena ya rike. An yi min haka ne domin na samu horo a kan kula da masu cutar kuturta da tarin fuka.

“A yanzu haka ina cikin shekara ta 12 a matsayin shugaban wannan asibiti. Alhamdulillah, na cim ma dukkan burukana domin kuwa baya ga samun nasarar jawo wutar lantarki zuwa kauyenmu, na kuma kawo mana wasu ayyukan ci-gaba kamar kwalta da dakin kwantar da marasa lafiya da rijiyar burtsatse.

“Haka kuma mafi yawan mazauna kauyen sun gina gidaje na zamani ba kamar da ba da muke zaune a cikin gidajen zana,” in ji shi.

Malam Umar ya kuma shaida wa Aminiya cewa, a yanzu haka cutar kuturta na raguwa a Jihar Kebbi sakamakon wayar da kai da ake yi wa al’umma a lungu da sakon jihar.

Ya ce, a yanzu mutane na kawo korafe-korafensu dangane da abin da ya shafi cututtukan fata ga likitoci domin daukar matakan da suka dace.

Ya ce, yin haka na taimakawa ainun wajen daukar matakan da suka dace a kan lokaci ba sai lamari ya ta’azzara ba. Sai dai Umar ya koka kan matsalolin da garin na Amanawa ke fama da su duk da nasarorin da aka samu wajen dakile cutar kuturta a jihar.

“Muna bukar kayan zamani a asibitinmu. Na samu horo a fannonin da dama na cututtukan da suka shafi kuturta, to amma rashin kayan aiki na zamani ba za mu iya aiwatar da wasu ayyukan ba.

“Haka kuma asibitin na bukatar a fadada shi domin a gina wasu fannonin da ba mu da su. Ka san shi fannin kiwon lafiya yana bukatar a rika fadada shi domin ya tafi da zamani.

“Bayan haka muna bukatar karin ma’aikata domin a yanzu haka mu 8 ne ke kula da asibitin, wanda ana bukatar akalla ma’aikata 15 domin kula da asibitin.

“Wannan shi ne asibiti tilo na masu fama da cutar kuturta a duk fadin jihar nan, kuma muna karbar marasa lafiya daga ko’ina a fadin jihar da makwabtan jihohi.

“Hakazalika muna bukatar ingantacciyar motar sufuri domin daukar marasa lafiya zuwa Jihar Sakkwato domin ba su kulawa ta musamman.

“Ko a makon jiya sai da na samu marasa lafiya mutum biyu wadanda matsalolinsu sun fi karfin matakinmu don haka sai na ce wa ’yan uwansu su kai su Sakkwato.

“Da a ce muna da motarmu kawai kai su za mu yi domin a kula da lafiyarsu,” in ji shi.

Shi ma da yake tattaunawa da Aminiya, Dagacin garin Amanawa, Malam Umaru Dagaci cewa ya yi wata babbar matsala da take addabar garin ita ce rashin gonakin noma, yana mai zargin cewa, Karamar Hukumar Kalgo ta karɓe duk gonakinsu ta mallaka wa wasu mutane.

“Ba mu da sauran gonakin noma a wannan kauye namu yanzu haka. Ka ga kuma wannan babbar matsala ce domin babu ta yadda za mu rayu babu noma.

“Gonakinmu duk an mallaka wa wasu mutane. Ba wai muna cewa gwamnati ta rika ba mu abinci ba ne, a’a mu dai a dawo mana da gonakinmu domin mu samu wurin noma abin da za mu ciyar da iyalanmu.

“Haka kuma muna bukatar magani a asibintinmu. Duk wanda ka gani a kauyen nan, to mai larurar kuturta ce ko wata cuta da shafi fata kuma ya zo ne domin karbar magani.

“Don haka in gwamnati ba ta samar da isasshen magani a asibitin ba, zamanmu a nan zai zama na banza domin kuwa dalilin kafa ƙauyen ya zama a banza,” in ji shi.

Malam Hashimu Bagudu daya daga cikin masu karbar magani a asibitin Amanawa ya shaida wa Aminiya cewa, an kwantar da shi a asibitin kimanin wata 6 da suka wuce kuma yana samun kulawar da ta dace daga ma’aikatan asibitin domin kuwa ana ba shi magani yadda ya kamata.

“Ina samun kulawa sosai a asibitin. Ina fama da kuraje da suka fito min a kirji.

“Na gode wa Allah kurajen sun fara mutuwa kamar yadda kake gani,” in ji Bagudu.

Wata mara lafiya, Binta Auwal daga garin Keita Fulani ta ce, “Na zo asibitin ne shekara ɗaya da ta wuce kuma ina samun kulawa sosai.

“Hasali ma lokacin da na zo asibitin ba na iya tafiya da kafafuna, amma yanzu ina tafiya kamar kowane mutum. Na gode wa Allah.

“Likitanmu na yin bakin kokarinsa wajen kulawa da ni. A da kafafuna duk sun fara rubewa, amma sakamakon kulawar da nake samu na fara samun sauki sosai idan aka yi la’akari da lokacin da na zo asibitin,” in ji ta.

Malam Umaru Falaha, wanda ya zo garin Amanawa shekara 15 da suke wuce ya ce, ya dawo garin ne tare da iyalinsa domin ba zai iya dawainiyar zuwa da komawa ba daga kauyensu.

“Muna kira ga Gwamna Nasir Idris na Jihar Kebbi ya kawo mana dauki domin muna cikin wani halin kaka-ni-ka-yi.

“Mafi yawan jama’armu ba sa iya ciyar da iyalansu sau uku a rana saboda halin da ake ciki na matsi.

“Muna bukatar abinci da sauran abubuwan more rayuwa. Gwamnatocin da suka gabata sun yi alkawarin taimaka mana, amma har suka sauka daga mulki ba su taimaka mana ba.

“A gaskiya ba ma son mu koma baracebarace. Kuma kamar yadda kake gani, ina yin wannan sana’a ce ta sakar zana don in samu abin da zan ciyar da iyalina kuma ina yin ta ce don ba na son yin bara,” in ji shi.

A bangaren Babban Limamin garin Amanawa, Malam Muhammad Dan Malam wanda ke zaune a kauyen shekara 35.

Ya bayyana takaicinsa kan yadda gwamnati ke tursasa kutare komawa barace-barace, inda ya ce gwamnati ta hana al’ummarsu damar noma sakamakon kwace gonakinsu.

Ya ce, “Za mu yi farin ciki idan har gwamnati ta ba mu horo a kan sana’o’i dabandaban domin tallafa wa rayuwarmu.

“Idan an ce mu mun tsufa, to, ai muna da ’ya’ya da idan an koya musu za su taimaki rayuwarmu.

“Muna sane da cewa Gwamnatin Tarayya da ta jihohi na ba da irin wannan tallafi ga al’ummomi da dama, amma abin takaici har yanzu ba a kula mu ba.”

Shi ma wani mazaunin garin, Ibrahim Muhammad ya ce, “A baya gwamnati na kawo mana magani da kayan abinci, amma yanzu an dakatar da haka.

“A yanzu sai dai mu tafi daji, mu saro itace, mu sayar don samun abin da za mu ciyar da iyalinmu. Idan ba ka je itace ba, to ba shakka za ka tafi bara domin ka samu abin da za ka ciyar da iyalinka.”