✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Amaryata ta haihu wata 3 da aurenmu’

Wasu iyaye kan hada baki da wasu malamai masu surkulle a kife ciki zuwa bayan aure a tayar da shi.

Wani ango ya bayyana halin da ya tsinci kansa bayan da amaryarsa ta haihu ’yan watanni da aurensu.

Mustafa Umar daga Zariya ya ce, ya bayyana wa shirin Aminiya na Daga Laraba, irin matukar kaduwa da mamakin a lokacin da ya gano yadda amaryarsa ta shigo masa gida dauke da cikin wani.

Angon ya shaida wa shirin cewa, “Bayan wata uku da kwana 14 da aurenmu, kwatsam sai na ji haihuwa! Abin ya taba mini zuciya da mamaki!”

Ya ce kyakkyawan zaton da yake da shi a kan maryar tasa ya sa tun farko bai yi tunanin za a samu wani akasi ba.

“Haihuwar da ta yi bayan wata uku da aure ya tada hankalin kowa a gidannmu, kuma hakan ya sa aka gano abin da ke faruwa,” in ji shi.

Binciken shirin Daga Laraba ya gano yadda a baya-bayan nan, matsalar ke faruwa a Arewacin Najeriya, inda ake samun amare na shiga gidan miji dauke da cikin wani.

Mustafa ya bayyana cewa, ba su taba aikata fasikanci ba kafin auren nasu balle a ce cikin nasa ne, “haka dai auren ya mutu dole.”

Abin da ke kawo matsalar

Da take tofa albarkacin bakinta kan wannan batu, wata uwa, Maryam Jibrin Kofar Bai ta ce, lallai wannan matsala ce da ke faruwa a cikin al’umma.

Ta ce, sakacin iyaye da rashin kamun kai daga bangaren yarinya na daga cikin dalilan da ke haifar da matsalar.

A cewarta, wasu iyayen kan hada baki da wasu malamai masu surkulle a kife cikin kafin aure har zuwa lokacin da ake bukata kafin a koma a tayar da shi.

Game da mafitar wannan matsalar, Maryam ta ce ya zama wajibi iyaye su kasance masu sanya ido sosai kan ’ya’yansu, musammam zirga-zirgarsu.

Ta nusar da iyaye kan duk wanda ya ga ’yarsu yana so, kamata ya yi ya shigo gida maimakon barin yarinya ta rika fita barkatai.