✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ambaliya ta halaka mutum 662, ta raba wasu miliyan 2.4 da muhallansu a 2022 – NEMA 

Hukumar ta ce za ta bullo da sabbin hanyoyin hana aukuwar iftila'in a gaba.

Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), Mustapha Habib Ahmed, ya ce akalla mutum 662 ne suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa a shekarar 2022 yayin da mutum 2,430,445 suka rasa matsugunansu a fadin Najeriya.

Ya ce kuma akalla mutum 3,174 kuma sun samu raunuka a yayin aukuwar iftila’in ambaliyar.

Ahmed ya yi wannan jawabi ne a ranar Litinin, a Abuja a wajen bude taron kara wa juna sani na mako guda ga ma’aikatan hukumar da kuma Cibiyar Kula da Iftila’i ta Jami’ar Bournemouth (BUDMC).

Shugaban, ya ce dubban gidaje da gonaki da kuma wasu muhimman kadarorin kasa sun lalace sakamakon ambaliyar ruwan, inda ya ce hukumar tare da gwamnatocin jihohi da sauran abokan hulda, na kokarin ganin an tallafawa al’ummar da abin ya shafa a fadin kasar nan.

Ya ce hukumar ta kawo kwararru da ke da gogewar aiki daga Birtaniya da kuma wasu kasashen ketare don tallafa wa gwamnatoci da kungiyoyi na kasa da kasa tare da samar da shirye-shiryen kan hana faruwar hakan a gaba.

Ahmed ya kuma bayyana cewa akwai yiwuwar sake fuskantar ambaliyar ruwa a bana amma bai da tabbacin yadda za ta kasance.

“Bayan wannan horon da kuma fitar da hasashen yanayi na NiMet da kuma hasashen ambaliyar ta NIHSA mun fitar da bayanin yadda abubuwa suke kuma za mu rubuta wa gwamnoni. Za mu zakulo wuraren da ke cikin hatsarin fuskantar ambaliyar,” in ji shi.

Ahmed ya jaddada hadin kai da gwamnatocin jihohi don magance ambaliyar ruwa da tasirinta a nan gaba.

“Na yi imanin cewa dole ne dukkan jihohi 36 su yi irin wannan kwas; su mayar da shi ga kwamitin kula da gaggawa na yankin da za su kafa.

“Dole ne mu shirya a kan lokaci. Mu shirya don hana sake faruwar irin abin da ya auku”.

A nasa bangaren, Daraktan Hukumar Kula da Albarkatun Jama’a, Musa Zakari, ya ce sauyin yanayi ne ya haifar da karuwar iftila’in a fadin kasar nan.

Ya ce hukumar na nazari kan wasu sabbin hanyoyin da suka dace don magance irin iftila’in da ambaliyar ruwan ta haifar.