✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliyar ruwa: mutum 100 sun mutu, sama da 1,000 sun bata a Jamus

A Jihar Rhineland-Palatinate da ke kasar kawai, akalla mutum 63 sun mutu.

Akalla mutum 100 sun mutu, sama da 1,000 sun yi batan dabo bayan wata mummunar ambaliyar ruwa a kasar Jamus.

Yankuna da dama dai sun shiga cikin halin kaka-nika-yi sakamakon ambaliyar da ta fara bayan wani mamakon ruwan saman da aka tafka.

Kazalika, iftila’in ya kuma jawo wata ambaliyar a makwabciyar kasar Jamus din wato Belgium.

Hakan dai ya jawo asarar rayuka akalla 12, yayin da suma kasashen Luxembourg da Netherlands ruwan saman ya shafe su.

A Jihar Rhineland-Palatinate da ke Yammacin Jamus kawai, akalla mutum 63 ne suka mutu, 43 kuma a makwabciyar Jihar Rhine-Westphalia, kamar yadda hukumomin kasar suka tabbatar.

Bugu da kari, kimanin mutum 1,500 ne a fadin kasar har yanzu ba a san inda suka shiga ba, a daidai lokacin da sojoji suka bazama wajen aikin ceto mutane.

Ministan Harkokin Cikin Gida na kasar, Herbert Reul, ya ce bai taba ganin annoba irin wannan ba a rayuwarsa.

“Lamarin fa ya yi muni matuka, ya fara zama abin tsoro,” inji Herbert yayin wani taron manema labarai.

Ya ce masu aikin ceto sun yi kokarin ceto kusan 30,000 a cikin ’yan kwanakin da suka gabata, ciki har da jigilar mutane ta jiragen sama daga asibitoci da kuma gidajen ba da agaji.