✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amira Souley: Tattaunawa da Gwarzuwar Hikayata ta 2022

Idan na yi Hausa sai ’yan Najeriya su fashe da dariya.

Wata matashiya mai suna Amira Souley Saluhu daga garin Maradi na Jamhuriyar Nijar ce Gwarzuwar Gasar Hikayata ta bana.

Labarin matashiyar mai taken ‘Garar Biki’ shi ne ya ciri tuta a gasar ta bana ta kagaggun gajerun labarai ta mata zalla da Sashen Hausa na BBC ya saba shiryawa duk shekara.

La’akari da cewa labarinta ne ya zo na daya a gasar, BBC ya bai wa Amira kyautar kudi har Dala 2,000.

A hirarta da Aminiya, Amira Souley Saluhu, ta ce ita haifaffiyar garin Maradi ce da ke Jamhuriyyar Nijar kuma shekarunta 24.

Ni malamar makaranta ce

Amira Souley ta ce ta yi karatun firamare da sakandare duk a cikin garin Maradi, inda a yanzu malamar makaranta ce a wata firamaren gwamnati a Maradin.

Ta ce ta yi karatun addini a cikin garin Maradi kuma har yanzu ba ta watsar da shi ba domin kuwa tana kan yi.

Na fi yin rubutu kan abin da ya shafi mata

Ta ce ita marubuciya ce musamman a kan kafafen sada zumunta, inda rubuce-rubucenta suka fi karkata kan abubuwan da suka shafi rayuwar mata.

A cewar gwarzuwar, galibin jigon rubuce-rubucenta sukan taba zukata, don mafi akasari masu karatu sukan zubar da hawaye duba da yadda rubuce-rubucen nata ke sosa zuciyarsu saboda shiga hali na jin tausayi.

Na nemi izinin maigidana kafin na fara rubuce-rubuce

Ta yi karin haske kan abin da ya ja hankalinta ta fara rubuce-rubuce, inda ta ce, “Gaskiya rubutu ba burina ba ne kuma ban taba tunanin zan iya zama marubuciya ba.”

Sai dai ta ce akwai wata rana tana zaune a gida sai wata kawarta ta kawo mata ziyara kuma suna tsakar hira sai ta kawo zancen su fara gwada rubutu ko watakila za su iya rubuta littafi.

A haka dai har kawar ta shawo kanta, amma Amira ta ce za ta yi shawara da mai gidanta, domin a lokacin tana da aure.

Nan take ya ce da ita to Allah Ya ba da sa’a kuma ta kira iyayenta ta sanar da su don a cewarta duk abin da mutum ya sanya gaba akwai bukatar ya nemi shawarar manya kafin ya shiga, inda ta yi sa’a suka karfafa mata gwiwa.

Daga nan ne ta fara rubutu tare da abokiyarta kuma sannu a hankali ta gano cewa ba a kirkirar marubuci rana daya illa iyaka baiwa ce da ake haihuwar mutum da ita.

“Na gano cewa ashe ni ma zan iya kuma cikin ikon Allah rubuce-rubucen nawa suka fara karbuwa wanda daga nan ne na zama marubuciya har na kawo wannan mataki.

‘Mayaudarin Masoyi’

Amira ta ce “Mayaudarin Masoyi” shi ne taken labarin farko da ta fara rubutawa, wanda ya tabo batutuwa kan samarin shaho wato samari masu yaudarar ’yan mata.

“Irin wadannan samarin da za su tunkari budurwa tamkar da niyyar aure har a amince da su su samu karbuwa a gidan wacce suka je wurinta.

“Sai budurwar ta gama yarda da su har an kai matakin fara shirye-shiryen aure amma sai su sulale a neme su a rasa.

“Dama da wata manufa ta su ta daban suka zo daga nan idan sun samu sun cimma hakarsu ko kuma asirinsu ya tonu an gane su sai su wanke kafafu su kara gaba.

“To wannan shi ne abin da labarin Mayaudarin Masoyi ya kunsa.”

Abin da ya sa na shiga Gasar Hikayata

Ta ce tun shekaru uku da suka gabata ta samu labarin gasar, amma sai a bara ta ce bari ta gwada sa’arta da labarinta mai taken “Sai A Lahira” kuma cikin sa’a labarin ya shiga cikin sahun 25 da aka zaba.

Bayan an yi bikin Gwarzuwar Hikayata na 2021 da mako guda, sai aka aika mata da satifiket na shaidar bajintar da ta yi, wanda hakan ya kara mata kwarin gwiwar cewa ita ma za ta iya tabukawa da gogayya a tsakanin marubuta.

Hakan ne dai ya sanya ta sake gwada sa’arta a gasar ta bana kuma cikin Kaddarawar Allah ta ciri tuta.

‘Garar Biki’

Ta ce ‘Garar Biki’ shi ne taken labarin da ta shiga da shi gasar a bana, wanda ya tabo yadda iyaye mata suka dauki al’adar Garar Biki suka mayar da ita kamar addini.

Ta ce, “Al’adar Gara a yanzu ta addabi al’ummar Hausawa don a duniya ba kowa ba ne ya dauke ta wani abu amma mu Hausawa mun dauke ta wani muhimmin abu.

“Don a wasu lokutan sai aure ya mutu, ko a fasa aure ko kuma ita wadda za a aurar ta shiga cikin tashin hankali ko iyayenta ko kuma tsakanin mata da miji a kasa samun zaman lafiya duk a dalilin gara.”

Ta ce wannan shi ne dalilin da ta rubuta labarin Garar Biki kuma a cikinsa akwai wani karamin jigo a cikin labarin wanda ta bayyana yadda ’yan mata suke tura wa samari hotuna da bidiyon tsiraicinsu.

Ta ce galibi matan sukan yi hakan ne saboda a tunaninsu tun da ba a wuri daya suke ba suna kwance ne a cikin gida to babu abin da zai taba mutuncinsu.

Ta ce wannan gurguwar dabara ce don sai an zo aure kuma asiri ya tonu a nan ne ido yake raina fata, wanda wani ma sai bayan shekaru da yin auren har an hayayyafa sannan a fito da bidiyon.

Wadannan su ne jigon da suka gina labarin “Garar Biki ”

Na yi farin ciki marar misali —Amira

“Yanayin da na tsinci kaina a lokacin da aka bayyana ni a matsayin Gwarzuwar Hikayata gaskiya ba zan iya misalta shi ba, don kuwa na shiga cikin farin ciki marar misali wanda kalamai na baka sun yi kadan su bayyana shi,” inji ta.

Ta yi godiya ga Allah don a cewarta Shi ne ya cancanci godiya da Ya ba ta wannan iko.

“Ba dabarata ba ce, eh, lallai na yi aiki tukuru kuma da karfin addu’a da yarjewa ta Ubangiji.”

‘Idan na yi Hausa sai a fashe da dariya’

Ta ce bayan fara rubuce-rubuce ta fuskanci kalubale na rashin daidaitacciyar Hausa, kasancewarta ’yar Nijar.

Ta ce bayan ta fara rubutu da Hausarsu ta Nijar don a tunaninta ita ma ai Hausa ce; “Idan na yi magana sai a fashe da dariya ko kuma idan na yi rubutu sai a ce ba a gane ba.”

Sai take mamakin yadda ’yan Najeriya suke mata dariya duk lokacin da ta yi Hausa, amma daga baya ta gano cewa a Najeriyar ce ake daidaitacciyar Hausa don su a Nijar Hausar baka kawai suke yi.

Wannan al’amari ya sanya ta ce za ta yi zuciya ta koya kuma ta rika mayar da hankalinta a duk wuraren da ta san za ta samu ci gaba a koyon Hausar don ita ta koma tana rubutu da kuma magana daidai gwargwado da irin Hausar da ake yi a Najeriya.

Ta ce tana godiya ga Allah da kuma ’yan uwanta marubuta wanda da taimakonsu ne ta kawo wannan matsayi a yanzu.

Ina son kawo sauyi a rayuwar mata

Amira ta ce babban burinta a fagen rubuce-rubuce shi ne kawo sauyi a cikin al’umma musamman a fannin rayuwar yan uwanta mata, don saboda “da za a bude zuciyata a yanzu, duk wani rauni a ciki ya samo asali da yadda mata suke rayuwa a yanzu.

Ina da burin na zama uwa

Matashiyar ta ce babban burinta a rayuwa shi ne ta zamo uwa kuma ta ga duk ta taka rawar gani wajen share hawayen duk wata mace da ke fuskantar kalubale kuma uwa uba ta ga farin cikin da annasshuwa a fuskar mahaifiyarta a kodayaushe.