✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Amurka ta jefa Najeriya cikin jerin kasashen masu hana walwalar addini

Gwamnatin Amurka ta jefa Najeriya cikin sahun kasashen da ke hana al’ummarsu walwala da rashin basu ’yanci a bangaren addini biyo bayan korafe-korafen da Kiristoci…

Gwamnatin Amurka ta jefa Najeriya cikin sahun kasashen da ke hana al’ummarsu walwala da rashin basu ’yanci a bangaren addini biyo bayan korafe-korafen da Kiristoci ke yi da nuna damuwarsu dangane da ci gaba da tabarbarewar matsalolin tsaro a kasar.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Mike Pompeo ne ya bayyana Najeriyar a matsayin kasar da ke tattare da matsaloli a bangaren addini wanda a cewarsa hakan ka iya tilasta su dauki mataki duk da kawancen da ke tsakanin kasashen biyu.

Mista Pompeo ya ce suna daukar mataki a kan irin wannan kasashen duniya da suka gaza shawo kan matsalar hana mutane walwala wajen gudanar da addininsu.

Sauran kasashen da Amurka ta sanya a jerin sun hadar da Cuba da Nicaragua da Sudan, yayin da kuma aka bayyana wasu kasashe masu wani abin damuwa mafi muni game da dakile ’yancin addini irin su Burma, China, Iran, Pakistan, Myanmar, Eritrea, Koriya ta Arewa, Saudiya, Tajikistan da kuma Turkmenistan.

Sanarwar da Amurka ta fitar dangane da dalilin da ya sanya Najeriya ta shiga sahun ta ce rikice-rikicen addini ya karu a bana, inda aka rika kaiwa Musulmai da Kiristoci hari a sanadiyar bangarancinsu na addini ko kabila.

Wani dalilin da sanarwar ta gindaya shi ne abin da ta kira take hakkin mambobin kungiyar IMN ta mabiya Shi’a, wanda shugabanta, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ke tsare tun a shekarar 2015 har kawo yanzu duk da cewa kotu ta ba da umurnin a sake shi.

Sai dai Gwamnatin Najeriya ta yi watsi da sanarwar Amurka na ayyana ta a cikin jerin kasashen duniya da suka gaza ta fuskar ’yancin addini.

Cikin wata sanarwa da ta fitar ta bakin Ministan Labarai da Al’adu, Lai Mohammed ranar Talata a birnin Abuja, ta bayyana lamarin sanya kasar a jerin a sakamakon rashin sanin hakikanin gaskiya da rashin fahimtar juna tsakanin kasashen biyu kan musabbabin tashin-tashinar da ke aukuwa a Najeriya.