✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amurka za ta tallafa wa Najeriya da wasu kasashen Afirka 9 da $215m su yaki yunwa

Najeriya na daga cikin jerin kasashen Afirka da za su ci moriyar tallafin

Kasar Amurka ta ce za ta bayar da Dala miliyan 215 a matsayin agajin gaggawa a wasu kasashen Afirka 10 domin shawo kan matsalar karancin abincin da su ke fuskanta.

Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken ne, ya sanar da haka lokacin da ya gana da wasu daga cikin takwarorinsa daga Afirka da suka halarci taro kan abinci na duniya a birnin New York.

Amurka ta ce matsalar ma barazana ga kasashen ne saboda illar sauyin yanayi, annobar COVID-19 da kuma yakin Ukraine.

Kasashen da ake sa ran za su amfana da tallafin na Amurka, sun hada da kasar Aljeriya, Burkina Faso, Mauritania, Kamaru da kuma Najeriya.

Sauran sun hada da Kenya, Rwanda, Uganda, Tanzaniya da kuma Zimbabwe.

A kwanan nan ne dai Sakatare-Janar na Majalisar Dunkin Duniya, Antonio Guterres, ya yi gargadin samun matsalar yunwa na tsawon lokaci, inda ya bukaci Rasha da ta ba da damar fitar da hatsin da ke kasar Ukraine domin samun sauki.

Guterres, ya ce a cikin shekara biyu kacal, mutanen da ke fuskantar matsalar karancin abinci sun ninka daga miliyan 135 a duniya zuwa miliyan 276, yayin da sama da 500,000 daga cikinsu ke fuskantar matsananciyar rayuwa.