✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An bankado ma’aikatan bogi 668 a Gombe

Ya ce sakamakon tantance ma'aikatan bogin, jihar ta adana Naira miliyan 38 da dubu 300.

Gwamnatin jihar Gombe ta ce ta bankado tare da korar ma’aikatan bogi 668 a saboda kin zuwa tantancewa tare da daukar hoton yatsun ma’aikatan dake gudana a jihar.

Kwamishinan Kudi da Ci Gaban Tattalin Arziki na jihar, Muhammad Gambo Magaji ne ya bayyana hakan ga ’yan jarida lokacin da aka kaddamar da tantance ma’aikatan a Akko.

Ya ce sakamakon tantance ma’aikatan bogin, jihar ta adana Naira miliyan 38 da dubu 300.

Muhammad ya ce an kaddamar da aikin ne a Kananan Hukumomin Akko da sauran Hukumomin Ilimi na Kananan Hukumomin.

“A Karamar Hukumar Gombe, kimanin ma’aikata 103 ne basu zo tantancewar ba, wadanda suka hada da na Karamar Hukuma 44 da kuma na ilimi 59, yayin da a Akko muka sami 134; ma’aikatan Karamar Hukuma 83 da na ilimi 51, kuma duk mun cire su daga kundin biyan albashin,” inji shi.

Kwamishinan ya ce za su ci gaba da tantancewar har sai sun kammala a dukkan Kananan Hukumomi tara na jihar.