An kashe wani dan bindiga a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja, bayan kwana biyu da ’yan bindiga suka yi garkuwa da Sarkin Bungudu da wasu matafiya a kan hanyar.
Wasu matafiya biyu kuma sun gamu da ajalinsu a musayar wutar da jami’an tsaro suka yi da maharan a safiyar Alhamis a kusa da kauyen Kasarami.
- An kama wadanda suka kashe dan Sanata Bala Na’Allah
- Idan Najeriya Ta Karbo Sabon Bashin Naira Biliyan 170,000
Wani shugaban matasa a yankin ya ce “Wani direban bas din haya da kwandastansa ne aka kashe da kuma wani dan bindiga” .
A cewarsa, ’yan bindigar sun lalata wata motar jami’an tsaro a lokacin da suke musayar wuta.
Mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kaduna, ASP Jalige Mohammed, ya tabbtar da faruwar lamarin.
Jalige ya kara da cewa jami’an tsaro sun dakile harin, inda suka kashe dan bindiga daya, amma wasu matafiya biyu sun rasa rayukansu.