✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An bukaci Gwamnati ta bankado ma’aikatun da ke rike kayan tallafi

Wajibi ne Gwamnati kada ta manta cewa da yawa daga cikin ’yan Najeriya sun rasa aikinsu.

Tsohon mataimakin sakataren yada labaran jam’iyyar APC na kasa Kwamared Timi Frank, a ranar Lahadi, ya yi kira ga hukumomin EFCC da ICPC masu yaki da yi wa tattalin arziki zagon kasa a Najeriya, da su bankado dukkan ma’aikatu da hukumomin gwamnati da aka kama su da hannu dumu-dumu rike da kayan tallafi da rage radadin zaman gida da gwamnati ta ware a lokacin kullen annobar COVID-19 da aka bayar don raba wa ‘yan kasa.

Kwamared Frank ya kuma yi kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya bayar da umarnin rarraba kayayyakin jin-kai da aka ware da kudaden da Gwamnatin Tarayya ta bayar don rabawa talakawa mabukata saboda rage radadin zaman gida na annobar Coronavirus.

A kwanaki biyun nan dai an samu wasu fusatattun matasa sun farfasa rumbunan ajiya na gwamnati a wasu jihohin kasar nan, inda suka rinka dibar kayayyakin abinci da sauran kayan rage radadin annobar Coronavirus da aka tanada.

Frank, ya bayyana haka ne a Birnin Tarayya Abuja, inda ya ce faruwar wannan lamari alama ce dake nuni da halin yunwa da matsanancin yanayi da ’yan Najeriya ke ciki a halin yanzu.

Ya yi kira da ire-iren ma’aikatun gwamnati da suka kulle irin wadannan kayayyakin tallafi a wuraren ajiye kaya, da su fito da su cikin gaggawa a raba wa talakawa mabukata.

Ya ci gaba da cewa “Lallai wajibi ne a kan Gwamnati da kada ta manta cewa da yawa daga cikin ’yan Najeriya sun rasa aikinsu da hanyoyin samun na-tuwo sakamakon bullar annobar Coronavirus.

“Muna son mu ji matsayin kudaden da aka karbo na tallafi daga cikin gida da kasashen waje, sannan akwai bukatar Shugaban Kasa lallai ya kafa kwamatin da zai bibiyi halin da kayan tallafin ke ciki.”