✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An cafke fasto kan sayar da ‘ruwa mai maganin bindiga’

’Yan sanda sun kama wani fasto da ke sayar da wani ruwan da ya yi ikirari yana maganin bindiga a Jihar Kogi.

’Yan sanda sun kama wani fasto da ke sayar da wani ruwan da ya yi ikirari yana maganin bindiga a Jihar Kogi.

Faston, wanda ke limanci a mujami’ar New Jerusalem Deliverence Ministry, ya shiga hannun ’yan sandan ne bayan bidiyonsa yana sayar da ruwan da ya ce yana magannin bindiga ya karade kafofin sada zumunta.

Kakakin Shugaban Karamar Hukumar Okene ta Jihar Kogi, Abdulmumini Abubakar, ya tabbatar wa wakilinmu gaskiyar labarin kama limamin cocin, mai suna Peter Michonza.

Jami’in ya ce, shugaban karamar hukumar ne ya umarci ’yan sandan su kama faston, su kuma gudanar da binciken kwakwaf a kansa.

Wani mazaunin unguwar Ageva inda cocin faston yake, ya ce, “Kowa ya san Michinza ne a matsayin mawaki, amma rana tsaka muka ji ya zama fasto, har yana bayar da magani.”

Mazauna unguwar suna kuma zargin sa da gudanar da aikin karbar haihuwa duk a cocin nasa.