✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ceto manoma 16 daga hannun masu garkuwa a Neja

An buɗe makarantun firamare da ke rufe tsawon shekaru a yankin saboda dalilai na matsalar tsaro.

Manoma 16 sun shaki iskar ’yanci bayan jami’an tsaro sun ceto su daga hannun masu garkuwa da mutane a kauyen Dan Gunu da ke Karamar Hukumar Munya ta Jihar Neja.

Shugaban Karamar Hukumar Munya, Abdulhamid Najume ne ya bayyana hakan yayin zantawa da wakilinmu ta wayar tarho a ranar Asabar.

Aminiya ta ruwaito cewa, a Larabar makon jiya ce ’yan bindiga suka kai hari kauyen na Dan Gunu, inda suka yi awon gaba da wadanda abin ya shafa ciki har da mata masu juna biyu da kananan yara.

A cewar Shugaban Karamar Hukumar, an samu nasarar ceto manoman ne bayan wani taron masu ruwa da tsaki kan sha’anin tsaro da aka gudanar.

Ya bayyana cewa hakan ce ta sanya aka bazama tare da bin sahun ’yan ta’addan, lamarin da ya kai ga ceto mutanen.

Ya kara ceto, mutanen da aka ceto na ci gaba da samun kulawa a asibiti domin tabbatar da lafiyarsu kuma daga bisani za su koma cikin ’yan uwansu.

Dangane da makarantun firamare da ke rufe tsawon shekaru a yankin saboda dalilai na matsalar tsaro, Najume ya ce an buɗe makarantun inda ɗalibai za su ci gaba da karatunsu.

Kazalika, ya ce an yi gyare-gyare a wasu daga cikin makarantun da aka buɗe domin ci gaba da harkokin karatu ba tare da wata tangarda ba.

“Mun rarraba kayayyaki kamar alli da littafan rubuta da sauran kayayyakin karatu musamman domin tallafa wa iyayen ɗaliban da ba su da halin ɗaukan wannan nauyi.”