✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ceto mata 4 daga hannun masu garkuwa a Zamfara

Matan sun kubuta bayan shafe mako uku a hannun ’yan bindiga.

’Yan sandan sun yi nasarar ceto mata hudu da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su sati uku da suka wuce a kauyen Bilbis a Karamar Hukumar Tsafe ta jihar.

Wannan na dauke ne cikin wani jawabi da kakakin ’yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu ya fitar a ranar Asabar.

  1. Buhari ya nada Obinna a matsayin sabon Shugaban PPPRA
  2. Darajar kwallayen gida da waje a gasar Zakarun Turai ta zama daya — UEFA

“Kwamishinan ’yan sanda, CP Hussaini Rabiu ya bayar da umarnin ceto matan cikin koshin lafiya.

“Bayan samun wasu bayanai a ranar 25 ga Yuni 2021, rundunar tsaro ta musamman ta yi nasarar ceto matan daga hannun wanda suka sace su.

“Dukkan wadanda aka ceto an duba lafiyar, an kuma yi musu tambayoyi kafin mika su ga iyalansu.

“Yanzu haka ana bincike don cafke wadanda suka yi garkuwa da su tare da gabatar da su gaban shari’a,” cewar sanarwar.