✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An ceto mata 9 daga hannun masu safarar mutane a Katsina

An nufi Nijar da matan inda daga za a tsallaka da su Libya.

Rundunar ’yan sandan Jihar Katsina ta ce ta samu nasarar ceto mutane tara da aka yi safarar su.

Kakakin rundunar, Gambo Isah ne ya bayyana hakan, inda ya ce bayanan sirrin da suka samu ne ya kai su ga ceto mutanen.

“Wadanda muka ceto sun hada da wani Timilaye Ojo da Safiyyat Ahmad ’yan asalin Jihar Legas, da Blessing Joseph daga Edo, da Khadija Abdullahi, da Taiwo Adeolo daga Ondo.

“Sauran sun hada da Precious Nuhu daga Jihar kaduna, sai Bolanle Adewusi daga Ogun, da Okpoekwu Eunice daga Jihar Enugu, sai Kabirat Azeez  daga Ondo”, in Kakakin.

Ya kuma ce yayin binciken, mutanen sun bayyana musu cewa an dauko su ne daga Jihar Kano suka biyo ta Daura ta Kwale-Kwale, inda suka nufi Nijar daga nan su tsallaka Libya.

Sai dai da hango jami’an tsaron masu safar tasu suka tsere suka bar su.

Isah ya ce suna ci gaba da bincike domin kamo masu safarar.