An ceto matashin da ’yan damfara suka yi yunkurin yi wa yankan rago a Kano | Aminiya

An ceto matashin da ’yan damfara suka yi yunkurin yi wa yankan rago a Kano

    Abubakar Muhammad Usman

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta ya yi nasarar kubutar da wani matashi daga hannun wasu ’yan damfara da suka yi yunkurin yi masa yankan rago.

Kakakin rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya sanar da hakan ga manema labarai a ranar Talata.

Kiyawa ya ce mutanen da ake zargin tuni suka fara yanka makogaron matashin, wanda jami’an ’yan sanda suka tserar.

Ya ce lamarin ya faru ne a cikin wani gida a Karamar Hukumar Dambatta a Kano.

Kiyawa ya ce tuni aka garzaya da shi babban asibitin garin na Dambata don ba shi kulawar gaggawa.

Matashin ya ce ya hadu da mutanen ne a kafar sada zumunta ta Facebook, da nufin za su yi kasuwanci.

Tuni aka mika wadanda ake zargin ga Sashen Binciken Manyan Laifuka da ke hedikwatar rundunar a Bompai.