✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ceto Shugaban APC da aka sace a Ekiti

Yanzu haka an kama mutane 3 da ake zargin suna da hannu wajen sace Mista Paul Omotoso.

Rundunar ’yan sanda a Jihar Ekiti ta sanar da ceto Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar, Mista Paul Omotoso da wasu mutane 2 da aka yi garkuwa da su kwanan baya.

Kakakin Rundunar ASP Sunday Abutu ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwar da ya fitar a wannan Juma’ar.

ASP Abutu ya bayyana cewa yanzu haka an kama mutane 3 da ake zargin suna da hannu wajen sace Mista Paul Omotoso da mutane 2 da aka yi garkuwa da su.

Ya ce an samu nasarar ce bayan rundunar hadin gwiwa ta jami’an tsaro da mafarauta sun rika fadi-tashin ceto wadanda lamarin ya rutsa da su lami lafiya ba tare da samun ko kwarzane ba.

“Yanzu haka suna tare da iyalan su a cikin gidajen su,” inji shi.

ASP Abutu ya ce rundunar ta baza komarta domin gano maboyar mutumin da ya jagoranci kitsa wannan aika-aikar.

Ya yi kira ga al’ummar Jihar Ekiti da su ci gaba da taimaka wa rundunar ta fannin bayar da labaran sirri da zai kai ga kama mutane masu aikata miyagun ayyuka a jihar.