✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An dage ranar dawo da ’yan Najeriya daga Ukraine

Najeriya ta dage kwaso ’yan kasarta da suka makale a Ukraine bayan barkewar yaki.

Gwamnatin Tarayya ta dage dawo da ’yan Najeriya da suka makale a Ukraine daga ranar Alhamis zuwa Juma’a.

Kawo yanzu dai babu wani dalili da gwamnatin ta bayar game dage ranar dawo da ’yan Najeriyan da suka makale a Ukriane, wadda Rasha ta far wa da yaki, mako guda yanzu.

A ranar Labara Ma’aiakatar Harkokin Wajen Najeriya ta sanar cewa rukunin farko na ’yan Najeriya da suka makale a Ukraine bayan barkewar yaki za su iso Najeriya a ranar Alhamis.

Sanarwar da Ma’aikatar da fitar a ta ce gwamnati ta tura jiragen kamfanin Max Air da Air Peace domin kwaso ’yan Najeriya mazauna Ukraine da suka yi kaura zuwa kasashen Poland, Romania da kuma Slovekia bayan barkewar yakin.

Hakan kuwa na zuwa ne bayan ’yan Najeriyan — kasar sauran ’yan sauran kasashe mazauna Ukraine — sun bukaci gwamnati da ta taimaka ta dawo da su gida, suna masu zargin jami’an Ukraine da fifita ’yan kasarsu a kan iyakar ficewa daga kasar.