✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An dakatar da Gwamnan Ekiti daga APC

Da alama rikicin da ke addabar jam’iyyar APC a Jihar Ekiti na dada kazancewa bayan da a ranar Juma’a shugabannin wani tsagin jam’iyyar a jihar…

Da alama rikicin da ke addabar jam’iyyar APC a Jihar Ekiti na dada kazancewa bayan da a ranar Juma’a shugabannin wani tsagin jam’iyyar a jihar suka sanar da dakatar da gwamnan jihar, Kayode Fayemi.

Kwamitin zartarwan tsagin jam’iyyar ya sanar da korar gwamnan bisa zarginsa cin amanar jam’iyyar da irin rawar da gwamnan ya taka a zaben gwamnan jihar Edo na makon da ya gabata wanda jam’iyyar ta fida.

A sanarwar ta ranar Juma’a dauke da sa hannun Sanata Tony Adeniyi da Sanata Babafemi Ojudu, shugabannin bangaren sun bayyana rawar da gwamnan ya taka a matsayin saba kundin tsarin mulkin jam’iyyar.

Sun yi zargin cewa kwanaki biyar kafin zaben Gwamnan Jihar Edo, Gwamna Fayemi ya karbi wasu jiga-jigan jam’iyyar adawa ta PDP a gidan gwamnatin jihar domin shirya abun da suka kira da ‘juyin mulki’ ga APC.

Kazalika, jam’iyyar ta zargi gwamnan da taka rawa wajen faduwar APC a zaben gwaman Jihar Oyo na 2019.

To sai dai a ranar Laraba, daya tsagin jam’iyyar a Jihar ta Ekiti ya sanar da korar Mai ba Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Siyasa, Sanata Babafemi Ojudu da wasu mutum 10 bisa zargin saba wa umarnin jam’iyyar.