✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An damfari matar Sarkin Bichi

Surukar Sarkin Kano, matar Sarkin Bichi ta maka abokin kasuwancinta a kotu kan damfarar kudin da ta zuba jari

Matar Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero, kuma surukin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ta fada tarkon damfara a hannun wani abokin kasuwancinta.

Hukumar yaki da masu yi wa arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta gurfanar da wanda ake zargin a gaban Mai shari’a Zuwaira Yusuf ta Babbar Kotun Jihar Kano, bisa zargin yin almundahanar kudi Naira miliyan 20.

Aminiya ta ruwaito cewa an gurfanar da Umar Bello Sadiq tare da kamfaninsa mai suna Marula Global Links Ltd, bisa zargin karbar Naira miliyan ashirin daga hannun Hajiya Faridah Nasir Bayero, uwargidan Sarkin Bichi, Nasir Ado Bayero, da sunan sanya hannun jari a kasuwancin ma’adinai.

Takardar karar ta bayyana cewa bayan Umar Bello da ake zargin ya karbi kudin, sai ya karkatar su don amfanin kansa, zargin da ya musanta.

Bayan wanda ake tuhumar ya musanta zargin ne lauyansa, Shu’aibu Muazu ya mika bukatar neman belin wanda yake karewa, shi kuwa lauyan masu shigar da kara Sadiq Kurawa ya roki kotun da ta dage zaman shari’ar.

Bayan sauraron bangarorin, Mai Shari’a Zuwaira Yusuf ta bayar da belin wanda ake kara a kan kudi N500,000 da kuma mutum biyu da za su tsaya masa guda biyu, bisa sharadin su kasance danginsa na jini.

Mai Shari’a Zuwaira Yusuf ta dage sauraron karar zuwa ranar 24 ga watan Nuwamba, 2023.