✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Peter Obi Ya Dauki Nauyin Bakanon Da Ya Mayar Da Tsintuwar N15m

An dauki nauyin karatun jami'ar matashin nan dan A Daidaita Sahu da ya mayar da Naira miliyan 15 da ya tsinta a babur dinsa

An dauki nauyin karatun jami’ar matashin nan da ke sana’ar haya da babur din A Daidaita Sahu, wanda ya mayar da Naira miliyan 15 da ya tsinta a babur dinsa.

Tsohon dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi da mataimakinsa, Datti Baba-Ahmed ne suka dauki nauyin karatun matashi mai suna Auwal Salisu.

Peter Obi da Datti sun dauki nauyin Auwalu mai shekaru 22 har sai ya kammala karatu a Jami’ar Baze mai zaman kanta da ke Abuja, inda za su rika biya masa kudin makaranta da na abinci da na dakin kwana da masa sauran bukatu.

Sun sanar da haka ne a taron karramawa na 2023 na LEADERSHIP 2023 da ke gudana a yau.

Auwalu mai shekaru 22 ya mayar da kudin da wani fasinjansa ya bari a cikin babur dinsa ne bayan da ya ji cigiyar kudin a gidan rediyo.

Wani dan kasuwa dan kasar Chadi da ya je Kano yin sayayya ne ya manta kudin nasa a cikin babur din Auwal, sai da matashin ya kai gidan iyayensa da ke unguwar ’Yankaba ya makudan kudaden.