✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An daure shi wata 4 kan satar ‘cingam’ a Abuja

Kotun ta ba shi zabin biyan tarar N10,000.

Wata kotu da ke zamanta a yankin Karu a Abuja, ta yanke wa wani mutum mai shekara 50, hukuncin zaman gidan yari na tsawon watanni hudu bisa samunsa da laifin satar fakiti biyu na cingam da kudinsa ya kai N12,840.

Mutumin da aka yanke wa hukuncin, wanda ke zaune a kauyen Garki, ya amsa laifin aikata satar.

Da yake yanke hukunci, alkalin kotun, Malam Ishaq Hassan, ya bai wa wanda ake tuhuma zabin biyan tarar Naira 10,000 sannan ya gargade shi da ya daina aikata laifuka.

Hassan ya kuma umarci wanda aka yanke wa hukuncin da ya biya diyyar N12,840.

Lauyan masu gabatar da kara, Mista Olarewaju Osho, ya shaida wa kotun cewa wanda ya shigar da karar, Joseph Sunday da ke aiki a babban shagon sayar da kayayyaki na Faxx Supermarket da ke Abuja, ya kai rahoton lamarin a ofishin ‘yan sanda na Durumi a ranar 7 ga watan Nuwamba.

Osho ya ce a ranar 18 ga watan Oktoba, wanda aka yanke wa hukuncin ya saci fakiti biyu na cingam “Orbit”, wanda kudinsa ya kai N12,840.

Ya ce tun lokacin da ‘yan sanda ke gudanar da bincike, wanda ake tuhumar ya amince da aikata laifin.

A cewarsa laifin ya saba sashe na 287 na kundin laifuffuka.