✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An daure ’yan Yahoo shekara 3 a Kano

Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke wa wasu masu danfara ta intanet wanda aka fi sani da harkar Yahoo hukuncin daurin shekara uku.

Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke wa wasu masu danfara ta intanet wanda aka fi sani da harkar Yahoo hukuncin daurin shekara uku.

Kotun, karkashin jagorancin Mai Shari’a Ibrahim Karaye, ta yanke wa Benjamin Udeagwu da Benjamin Olamide hukuncin ne a ranar Laraba bayan Hukumar EFCC ta gurfanar da su.

Kowanne daga cikin mutanen biyu da aka yanke wa hukuncin sun amsa lafin nasu kafin kotun ta yanke musu hukuncin zaman gidan yari na shekara uku.