✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An fatattaki Southampton daga Firimiyar Ingila bayan shekara 11

Ya rage wa Southampton wasanni biyu kacal a gasar Firimiyar bana.

Southampton ta zama kungiya ta farko da ta koma rukunin ‘yan dagaji wato relegation a gasar Premier League ta Ingila.

Hakan na zuwa ne bayan da ta sha kaye a hannun Fulham da ci 2-0, lamarin da ya bar kungiyar da maki 24 kacal cikin 36 da fafata a gasar ta bana.

‘Yan wasan Fulham Carlos Vinicius da Aleksandar Mitrovic ne suka ci wa kungiyar kwallayenta.

A kakar wasanni ta 2012/2013 Southampton ta samu nasarar haurowa zuwa gasar Firimiya, inda a yanzu ta shafe shekara kusan 11 ana fafata gasar da ita.

Duk da ta fice daga gasar ta Firimiya, ya rage wa Southampton wasanni biyu.

Firaiministan Birtaniya, Rishi Sunak wanda masoyin kungiyar ta Southampton ne, ya halarci wasan da ya kai ga ficewar ta daga gasar.