✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Musulumi ya sanar da ganin watan Ramadan a Najeriya

Sarkin Musulmi ya tabbatar da ganin watan Ramadan a Sakkwato, Borno, Katsina, Filato, Kano, Kaduna, Zamfara da Yobe

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar, ya bayar da sanarwar ganin watan Ramadan na shekarar 1443 Hijiriyya a Najeriya.

Sarkin Musulmi ya sanar da ganin watan ne a ranar Juma’a, 1 ga Afrilu, 2022, da dare a fadarsa da ke Sakkwato.

“Mun aminta da sahihancin labarin ganin watan da aka yi a jihohin Sakkwato, Borno, Katsina, Filato, Kano, Kaduna, Zamfara da Yobe,” inji Sarkin Musulmi.

Ya tabbatar da samun labarin ganin watan daga shugabanni addini da kungiyoyi daban-daban a Najeriya.

Duk da cewa bai zayyano garuruwan da aka ga watan ba, Sarkin Musulmi ya ce kwamitin ganin watan ya tantance sahihancin duk bayanin da aka samu kafin a kawo maganar gabansa.

Hakan ke nuni da cewa watan sha’aban na shekarar 1443 Hijiriyya ya kawo karshe, Assabar 2 ga Afrilu, 2022 za ta zama ranar 1 ga watan Ramadan, 1443 Hijiriyya.

Sarkin ya roki Musulmi su yaiwata addu’a a cikin watan Ramadan domin kawo karshen matsalar rashin tsaro da ta addabi Najeriya.

Ya yi kira ga mawadata su taimaki talakawa a watan ba tare da kula da bambancin siyasa da kabila ba.

Sakon nasa ya kuma yi kira ga shugabbani da su kara dagewa wajen ganin sun yaki matsalar tsaro da ake fama da ita, sannan jama’a su ci gaba da yi wa kasa addu’a don samun cigabanta.