✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ga watan Ramadan a Saudiyya

Ranar Litinin za ta zama 1 ga watan Ramadan na shekarar 1445 bayan hijira a Saudiyya.

Rahotanni daga Kasar Saudiyya sun tabbatar da ganin jinjirin watan azumin Ramadan na bana a sassa daban-daban na kasar a ranar Lahadi.

Hakan dai na nufin ranar Litinin ce, za ta kasance daya ga watan Ramadan na shekarar 1445 bayan Hijira, wacce ta yi daidai da 11 ga watan Maris 2024.

Hakan na zuwa ne bayan watan Sha’aban ya cika kwana 29, inda dama watannin Musulunci ba sa wuce kwana 29 zuwa 30.

Al’ummar Musulmai a fadin duniya dai kan azumci tsawon Ramadan, wanda shi ne wata na tara a kalandar Musulunci, inda suke kauracewa ci da sha da kuma saduwa da iyali tun daga fitowar rana har zuwa faduwarta.

Kazalika, azumi na daya daga cikin shika-shikan addinin Musulunci guda biyar.

A halin yanzu dai a Najeriya ana jiran dakon sanarwa daga Fadar Sarkin Musulumi, Muhammad Sa’ad Abubakar III, game da ganin watan na Ramadan.