An ga watan Babbar Sallah a Saudiyya | Aminiya

An ga watan Babbar Sallah a Saudiyya

Wata
Wata
    Sagir Kano Saleh

Kasar Saudiyya ta ga jinjirin watan Dhul Hajji a ranar Laraba, 29 ga watan Yuni, 2022 wanda ya zo daidai da 29 ga watan Dhul Kida, 1443 Bayan Hijira.

Shafin Masallacin Harami na Saudiyya ne ya sanar da haka, tare da bayyana cewa mahajjata za su yi tsayuwar Arfa a ranar Juma’a, 8 ga watan Yuli, 2022.

Hakan na nufin ranar Alhamis 30 ga watan Yuni, zai kasance 1 ga watan Zul Hajji a kasar Saudiyya.

A ranar Asabar 9 ga watan Yuli kuma za a yi Babbar Sallah a Saudiyya, kuma ranar da alhazai za su fara jifa da kuma yanka dabbobinsu na Hadaya a Kasa Mai Tsarki.