✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gano gawar Palasdinawa 210 da Isra’ila ta kashe a asibitin Gaza

Hukumomi a Zirin Gaza sun tono gawarwakin Palasdinawa sama da 210 da Isra'ila ta kashe daga wani katon kabari da ta gano a asibitin Nasser…

Ma’aikatan tsaron fararen hula a Zirin Gaza na ci gaba da tono gawarwakin mutane daga wani katon kabari da ta gano a asibitin Nasser da ke yankin Khan Younis.

Wata matar aure mai suna Umm Mohammed al-Harazeen na daga mutanen da suka je asibitin cike da fatan samun labarin mijinta.

Magidancin ya bace ne tun lokacin da sojojin Isra’ila suka fara shiga Khan Younis a watannin da suka gabata, kuma har yanzu babu labarinsa.

Kungiyar fafutukar kare hakkin Falasdinu ta Amurka ta yi tur da kisan kiyashin da sojojin Isra’ila suka yi wa Palasdinawa.

“Wadannan kaburburan jama’a da ake ganowa shaida ne a fili kan kisan kiyashi da kuma laifukan yaki marasa misali,” da Isra’ila ta aikata, in ji kungiyar.

Ta bayyana cewa labarin kashe dimbin jama’a da aka yi a Khan Younis ya zo ne a daidai lokacin da Majalisar Wakilan Amurka ta amince da bayar da dala biliyan 14 na taimakon soji “a yayin da Isra’ila ke barazanar kai hari ta kasa don kashe Falasdinawa a Rafah”.

Tarayya Turai (EU) ta yi kira ga Isra’ila da babbar murya cewa kada su kai hari Rafah, su kare fararen hula.

Babban jami’in harkokin wajen EU, Josep Borrell, ya yi kiran ne a lokacin taron majalisar kula da harkokin waje ta EU.

Ya ce, “Akwai fiye da mutane miliyan 1, wadanda za a kashe su idan aka kai hari daga Isra’ila.

“Don haka, duk mambobin EU na kira da kada rundunar sojin Isra’ila ta kai harin.”

Kiran na EUnna zuwa ne bayan Ministan Harkokin Wajen kasar Jordan, Ayman Safadi, ya yi kira ga duk masu fada a ji da su matsa lamba wajen ganin sojin Isra’ila ba su kai harin a Rafah ba.

A cewarsa ta X “harin zai zama wani ƙarin kisan kiyashi ne.”