✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gurfanar da tsohuwar Ministar Man Fetur Diezani Alison-Madueke a Birtaniya

A shekarar 2015 ne aka kama Diezani a birnin Landan, jim kaɗan bayan sauka daga muƙamin minista.

Tsohuwar Ministar Man Fetur ta Najeriya, Diezani Alison-Madueke ta gurfana a gaban wata kotu da ke birnin Landan bisa zargin ta da ayyukan rashawa.

Madueke wadda ta gurfana a kotun yau Litinin, ana tuhumar ta ne da karɓar cin hanci na kuɗi da kayan ƙawa da amfani da jiragen sama na alfarma da kuma yin rayuwa irin ta hamshaƙan masu kuɗi a Birtaniya.

Ana zargin cewa ta karɓi waɗannan abubuwa ne a matsayin cin hanci domin ta bayar da kwangilolin da suka shafi man fetur.

Diezani Alison Madueke ta riƙe muƙamin minista ne ƙarƙashin mulkin tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan tsakanin shekarar 2010 zuwa 2015.

A lokacin da ta gurfana a gaban kotun a yau Litinin, ta yi magana ne kawai domin tabbatar da sunanta da kuma adireshinta.

Ba a yi mata tambaya a kan ko ta amsa laifin ko kuma a’a ba, ko da yake dai lauyanta ya shaida wa kotun cewa ba za ta amsa laifin ba.

Diezani ce ta biyu a cikin mutanen da suka taɓa riƙe wani babban muƙami a Najeriya, da suka gurfana gaban kotu a Birtaniya cikin shekarun nan bisa zargin ayyukan rashawa.

A shekara ta 2015 ne aka kama Diezani Madueke a birnin Landan, jim kaɗan bayan sauka daga muƙamin minista, inda aka gurfanar da ita a kotu kan laifuka shida waɗanda suka jiɓanci rashawa.

Ta kwashe shekara takwas ɗin da suka gabata a ƙarƙashin beli a wata unguwa da ke birnin Landan.