✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gurfanar da ’yan bangar siyasa 10 a Sakkwato

Kwamishinan ’yan sandan jihar ya gargadi ’yan siyasa da hana magoya bayansu daukar da makamai yayin yakin neman zabe.

Rundunar ’yan sandan Jihar Sakkwato ta ce ta gurfanar da wasu mutum 10 da ake zargin ’yan bangar siyasa ne a gaban kotu.

Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Sanusi Abubakar, ya bayyana a ranar Litinin, cewa an kama su ne bayan umarnin kwamishinan ’yan sandan jihar, Muhammad Gumel.

“Ya bayar da umarnin shiga lungu da sako, musamman ofisoshin ’yan siyasa da ofishoshin yakin neman zabe don dakile ’yan bangar siyasa.

“’Yan sanda da hadin guiwar sauran jami’an tsaro sun shiga wuraren da ake kyautata zaton akwai wadanda suke tada tarzoma a jihar.

“Wadanda ake zargin an kama su da muggan makamai, layu da kuma miyagun kwayoyi a tare da su,” a cewarsa.

Ya kara da cewa Kwamishinan ’yan sandan jihar, ya gargadi ’yan siyasa da su ja kunnen magoya bayansu kan amfani da makamai a lokutan yakin neman zabe.