✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gwangwaje ’yan gudun hijira 7,500 da kayan tallafi a Kano

Hukumar za ta kuma gina wani birni mai gidaje 600 ga mutanen da suke cikin tsananin bukata a jihar.

Kwamishinan Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Kasa, Sanata Bashir Garba Lado a ranar Lahadi ya kaddamar da raba kayan tallafi ga iyalai 1,500 da ya kunshi ’yan gudun hijira 7,500 a jihar Kano.

Lado ya ce hukumar za ta kuma gina wani birni mai gidaje 600 ga mutanen da suke cikin tsananin bukata daga cikin ’yan gudun hijirar a jihar.

Ya ce gine-ginen dai ana sa ran za su kunshi gidaje masu dakuna bi-biyu, dakin shan magani, makarantu domin inganta harkokin ilimi, cibiyoyin koyar da sana’o’i, wuraren motsa jiki, ruwan sha, ofisoshin jami’an tsaro da kuma hanyoyi.

A yayin bikin dai, Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayar da takardar mallakar filaye masu fadin hekta 20 domin fara aikin gina gidajen.

Gwamnan ya kuma ce gwamnatinsa ta damu matuka da walwalar mutanenta, dalilin kenan da yasa za ta tallafawa yunkurin na Gwamnatin Tarayya ta hanyar bayar da kyautar filayen da za a gina gidajen.