✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An harbi dan banga, an sace mutum 3 a Abuja

Maharan sun yi awon gaba da wasu mutum uku a yankin Bwari

’Yan bindiga sun harbi wani dan banga mai suna Samson tare da raunata wasu mutum uku a yankin Barangoni da ke Karamar Hukumar Bwari a Yankin birnin Tarayya.

Wani mazaunin Barangoni mai suna Joshua Madaki, ya ce lamarin ya faru ne a safiyar Litinin, inda ’yan bindigar suka mamaye yankin.

Ya ce ’yan bindigar sun kai farmaki ne gidan wani Ishaya Markus, inda suka yi awon gaba da mutum uku.

Ya ce ’yan banga da ke sintiri a yankin sun kai dauki, amma daya daga cikin ’yan bindigar ya bude wuta, ya raunata dan banga daya.

Ya ce dan bangar ya samu rauni a cinyarsa amma an garzaya da shi asibiti a yankin domin yi masa magani.

Yankin Karamar Hukumar Bwari na fuskantar hare-haren ’yan bindiga a baya-bayan nan.

Kakakin ’yan sandan Babban Birnin Tarayya, Abuja, SP Adeh Josephine, ba ta ce komai a kan harin ba.

Kazalika, ba ta ba da amsar sakon waya da aka aike mata ba, har aka kammala hada wannan rahoto.