✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kafa dokar hana acaba da haya da Keke Napep a Kogi

Dokar za ta fara aiki daga ranar Litinin 17 ga watan Janairu, 2022.

Gwamnatin Jihar Kogi ta fito da sabuwar dokar hana zirga-zirgar Keke Napep da kuma yin acaba a kan manyan titunan Lokoja, babban birnin Jihar.

Gwamnatin dai ta sanya ranar Litinin 17 ga watan Janairu a matsayin ranar da dokar za ta fara aiki.

Aminiya, ta gano an gudanar da taron masu ruwa da tsaki a Jihar kafin zartar da hukuncin, kan yadda ake samun yawan hatsari a birnin.

Taron da ya gudana a tsakanin wakilan gwamnatin Jihar da kuma shugabannin kungiyoyin masu Keke Napep da ’yan acaba sun amince kan hukuncin da gwamnatin ta dauka.

A cewar kwamishinan sufurin Jihar, Baron Joseph Okwoli, taron ya shirya samar da hanyar ci gaba da rage hatsari a cikin gari.

Kazalika, Kwamishinan ya ce gwamnatin Jihar ta bukaci kungiyar matuka baburan Keke Napep da ta mika jerin sunayen matuka baburan da ke fadin Jihar don tantace su.

“Kowane Keke Napep dole ne a tantance shi tare da fitar masa da lamba ta musamman da zai rika aiki da ita.

“Kuma dole ne a yi wa masu acaba doka kan adadin mutanen da za su dauka,” a cewar Kwamishinan.