✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kai hari gidan Sunday Igboho

’Yan bindigar da suka kai harin sun yi shiga irin ta kakin sojoji.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu ’yan bindiga sun kai hari gidan dan gwagwarmayar nan mai rajin kare hakkin Yarbawa, Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, ’yan bindigar sun kai hari gidan ne da misalin karfe daya na daren ranar Alhamis.

Bayanai sun ce ’yan bindigar da suka kai harin sun yi shiga irin ta kakin sojoji, inda yayin harin suka lalata dukiya ta miliyoyin naira a gidan da ke yankin Soka a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.

Wani bidiyo da ake ta yadawa a dandalan sada zumunta, ya nuna yadda aka lalata wasu motoci na alfarma a gidan da kuma sauran kayayyaki masu daraja.

Haka kuma, wakilinmu da ya kai ziyara gidan ya tarar da yadda harsashan bindiga suka yi wa motocin fatata sannan kuma da alamun jini da ya zuba a harabar gidan.

Sai dai bincike ya nuna Igboho bay a gidan a lokacin da lamarin ya faru.

Aminiya ba za ta iya tabbatar da faruwar lamarin ba, a yayin da rundunar ’yan sandan Jihar ba ta ce uffan a kansa ba.