✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kai harin kunar bakin wake a sansanin sojin Mali

Gwamnatin Mali ta ce an kai harin kunar bakin wake mai ban mamaki a sansanin sojinta a yankin Gao

Gwamnatin sojin kasar Mali ta ce an kai harin kunar bakin wake a wani sansanin sojinta a safiyar Juma’a.

Gwamnatin da ke kokarin murkushe ’yan ta’adda ta ce akwai sarkakiya a harin kunar bakin wake da aka kai kusa da filin jirgi da ke sansanin sojin a yankin Gao da ke Arewacin kasar.

Zuwa yanzu dai gwamnatin ba ta yi karin haske kan harin kunar bakin waken ba.

An kai sabon harin ne washegarin da ’yan ta’adda suka kai hare-hare kan wani sansanin soji da wani jirgin ruwan fasinja, suka kashe sojoji da fararen hula 64 a Arewacin kasar a ranar Alhamis.