✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama basarake kan zargin yi wa yaro mai shekara 14 fyade a Zariya

Kusan shekara 20 ke nan da aikata laifin

Rundunar ’Yan Sandar Jihar Kaduna ta tabbatar da kamawa tare da tsare Shehu Umar, mai rike da sarautar Chiroman Barayan Zazzau bisa zargin yi wa wani yaro mai shekara 14 fyade.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandar Jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige, ya tabbatar da kamun a zantawarsa da manema labarai a Zariya.

Jalige ya ce ’yan sanda na ci gaba da binciken lamarin kuma ya ce da zarar sun kammala bincikensu za su gurfanar da shi a gaban kotu.

Rahotanni daga mazauna anguwar na nuni da cewa dama mutane na zargin basaraken da aikata wannan laifin kusan shekaru 20 da suka gabata.

Aminiya ta zanta da dan uwan yaron da aka yi wa fyaden, wadda ya ce ya ce lamarin ya faru ne a gidan mai sarautar da ke unguwar Kwarbai cikin birinin Zariya.

Zubairu ya kara da cewa kasantuwar yaron makwabcin basaraken ne, kuma yaron na daukarsa a matsayin uba, sai basaraken ya aike shi dakinsa don ya dauko masa kudi.

Ya ce sai dai bayan shigar yaron dakin, sai basaraken ya biyo shi a baya ya rufe kofa ya dauki wuka ya ce zai kashe shi idan ya yi ihu, sannan daga bisani ya aikata mummunan aikin ga yaron.

Ya ci gaba da cewa yaron ya dimauce bisa abin da ya faru da shi, inda ya je ya sanar da kanwar mahaifiyarsa inda ita kuma ta sanar da su.

Dan uwan yaron ya ce jin haka ne ya sa suka tara ’yan uwa don daukar matakin
kai kara ofishin yanki na ‘’yan sanda na cikin birnin Zariya.

Wakilin Aminiya ya garzaya sashin kula da cin zarafin mata da yara na asibitin Gambo Sawaba da ke Zariya, inda aka yi gwaje-gwaje kan yaron.

Shugabar Sashen, Hajiya Aishatu Ahmed, ta tabbatar da cewa, “Jami’an ’yan sanda da ke Fada, Zariya sun kawo yaron don a duba lafiyarsa, tare da wadda ake zargin ya aikata fyaden kuma mun bai wa ’yan sanda sakamakon bincikemmu,” inji ta.