✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama dan kasar waje yana garkuwa da mutane a Najeriya

Yana zuwa ne daga Jamhuriyar Benin domin garkuwa da mutane daga kasa zuwa kasa.

Jami’an tsaro sun cafke wani dan kasar waje da ke shigowa Najeriya domin yin garkuwa da mutane.

’Yan sanda sun cafke mutumin, wanda dan asalin kasar Jamhuriyar Benin ne, a Dajin  Kosubosu da ke Karamar Hukumar Baruten ta Jihar Kwara, dauke da muggan makamai da kuma tsabar kudi Naira miliyan 2.3.

“Wanda ake zargin ya amsa cewa shi dan wani gungun wasu masu garkuwa da mutane ne a tsakanin kasa da kasa da ke Jamhuriyar Benin,” a cewar sanarwar da Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kwara ta fitar.

Sanarwar da kakakin rundunar, Ajayi Okasanmi, ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa ’yan banga ne suka taimaka wajen cafke mutumin, wanda aka kwace wasu wayoyin hannu a hannunsa, a Dajin Kosubosu da ke Karamar Hukumar Baruten ta jihar.

Ya kara da cewa nan gaba za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kuliya da zarar rundunar ta kammala bincike.