✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘An kama fasto ya yi wa ‘yar shekara 12 fyade’

Wani dan shekara 54 ya shiga komar ‘yan sanda bayan zargin sa da yi wa yarinya ‘yar shekara 12 fyade a jihar Ogun. Mahaifin yarinyar…

Wani dan shekara 54 ya shiga komar ‘yan sanda bayan zargin sa da yi wa yarinya ‘yar shekara 12 fyade a jihar Ogun.

Mahaifin yarinyar ya yi karar mutumin, mazaunin Itele Ota a jihar Ogun ne bayan makwabta sun sanar da shi cewa ya lalata diyarsa.

Kakakin ‘yan sandan jihar Ogun DSP Abimbola Oyeyemi ya shaida wa Aminiya cewa, “Wanda ake zargin, wanda ya ce shi fasto ne, ya ce ya lalata yarinyar ne a cikin wani kango bayan ya yaudare ta a lokacin da ya gan ta tana yawo”.

Abimbola ya ce mutumin da ya ce shi fasto ne a cocin Helmet Life, “Ya rabu da matarsa tun a shekarar 2016”, kuma bayan bincike za a gurfanar da shi a kotu.