✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama lakcara kan lalata da dalibansa don ba su maki a Yobe

Asirinsa ya tonu bayan ya yi wa wata fyade a cikin ofishinsa da ke babban asibitin Potiskum.

’Yan sanda sun tsare wani malami da ke yi wa dalibansa fyade domin ba su maki a wata kwalejin kimiyyar lafiya a Jihar Yobe.

Dubun malamin ta cika ne bayan ya yi wa akalla daibai mata hudu fyade a Kwalejin Kimiyyar Lafiya ta Al-Ma’arif mai zaman kanta da ke Karamar Hukumar Potiskum a jihar.

Malamin da ake zargi ma’aikaci ne kuma a Babban Asibitin Potiskum, inda yake zuwa koyarwar wucin-gadi a kwalejin koyon aikin jinyan da yake wa dalibai fyade domin ba su maki.

Aminiya ta gano cewa asirinsa ya tonu ne bayan da ya yi wata fyade a cikin ofishinsa da ke babban asibitin.

Dalibai mata a kwalejin sun kuma kai kara kan yadda ya yi wa dayarsu fyade da kuma yadda yake yaudararsu ya yi lalata da su domin ba su maki.

Kakakin ’yan sandan jihar Yobe, DSP Dungus Abdulkareem, ya tabbatar da cewa rundunar na binciken lakcran da ke tsare a hannnunta kan zargin yin lalata da dalibansa a makarantar da kuma a asibiti.

DSP Dungus ya ce akalla dalibai hudu be ake zargin malamin ya lalata da sunan ba su maki.

A cewar jami’in ya ce rundunar tana ci gaba da gudanar da bincike kuma idan ta kammala za ta gurfanar da shi a gaban kuliya.