✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama magidancin da ya yi wa ’yarsa fyade

Budurwar ta ce mahaifin nata ya far mata da karfin tsiya ya kuma zakke mata.

’Yan sanda sun cafke wani magidanci bisa zargin sa da yi wa ’yar cikinsa mai shekara 13 fyade.

Yarinyar da aka yi wa fyaden ce da kanta ta kai karar mahaifin nata ga Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ogun, inda ta fede wa jami’an Rundunar biri har wutsiya.

Bayan bayanin da yarinyar ta yi na irin aika-aikan da ta ce mahaifin nata ya yi mata, sai DPO na Obantoko, Sunday Opebiyi, ya tura jami’ansa suka je suka taso keyar magidancin.

A ranar Larabar da ta gaba ce budurwar ta shaida wa caji ofis din Obantoko da ke Abeokuta cewa mahaifinta ya je kantin da take koyan dinki ya nemi izinin a bari ta debo masa ruwa saboda ba su da ruwa a gida.

Bayan ta gama diban ruwan ne, kafin ta ankara sai kawai mahaifin nata ya far mata da karfin tsiya ya kuma zakke mata.

Kakakin ’yan sandan Jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya shaida wa Aminiya a ranar Talata cewa, mutumin “da farko ya musanta zargin, amma da suka yi ido hudu da ’yar tasa sai ya fara kame-kame.”

Oyeyemi ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Edward Ajogun ya ba da umarnin a Sashen Bincikne Manyan Laifuka na Rundunar su zurfafa bincike a kan lamarin.