✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama mai yi wa Boko Haram leken asiri a Yobe

A kama mutumin ne Timbuktu, wani bangare mai sarkakiya a dajin Sambisa da yankunan kusa da Tafkin Chadi.

Rundunar sojin kasan Najeriya ta sanar da cewa dakarunta na Operation Lafiya Dole, sun cafke wani mai yi wa mayakan Boko Haram leken asiri a Jihar Yobe.

Ana zargin ayyukan leken asirin ne suka taimaka wajen hare-haren da ake kai wa sojoji a yankin Kamuya na Jihar Yobe.

Wata sanarwa da kakakin rundunar sojin kasa, Birgediya-Janar Mohammed Yerima ya fitar a ranar Lahadi, ta ce dakarunsu da ke Bataliya ta 27 ce suka cafke mutumin mai suna Modu Ari.

Birgediya-Janar Yerima ya ce binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa mutumin yana leken asiri ne a kan ayyukan dakarun sojin da zummar kaddamar da hari a kansu ba tare da samun wata tangarda ba.

“A yanzu haka za mu ci gaba da bincike domin bankado ragowar masu taimaka masa wajen yin leken asiri a kan ayyukan dakarunmu.

“Wannan leken asiri da ake yi yana jefa dakarunmu cikin hadari musamman a yankunan Timbuktu,” a cewar sanarwar.