✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama mutum 18 kan zargin aikata fyade a Borno 

An kama mutanen ne a sassa daban-daban na Jihar

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno ta kama wasu mutum 18 da ake zargi da aikata laifukan fyade, lalata da kuma mallakar muggan makamai.

An kama mutanen ne a Maiduguri, babban birnin Jihar da kuma Karamar Hukumar Jere a cikin makonni biyun farko na watan Janairun 2023.

Da yake gabatar da wadanda ake zargin, a Maiduguri, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Abdu Umar, ya bayyana wa masu laifin cewa, “Ko da kun tuba daga kama ku dole ne ku fuskanci fushin hukuma.

“Babu wani mutum ko gungun mutane da aka yarda su keta hakkin wasu, musamman a kan abubuwan da suka hada da ’yancin rayuwa da na mallakar wasu mutane,” in ji shi.

Kwamishinan ya kuma, “Akwai Abdullahi Mohammed, a ranar 18 ga watan Janairu, 2023, jami’an ’yan sanda na Crack Operatives sun kama shi ne bisa samun labarin satar wani injin sarrafa hasken rana da aka kiyasta kudinsa ya kai Naira miliyan biyu.

“A yayin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa cewa ya sace injin ne a wata rijiyar burtsatse mai amfani da hasken rana tare da wani mai suna Musa Ajakuta da ke kauyen Njimtilo.”

Ya kara da cewa wadanda ake zargin sun kuma lalata tashar iskar gas mai karfin megawatt 50 da ke a Maiduguri.

A cewarsa, duk ta’asar da wadanda ake zargin suka aikata, ana kan yin bincike a kansu, kuma da zarar an kammala za a gurfanar da su a gaban kotu.

Baya ga haka, Kwamishinan ya ce jami’ansa sun kuma kama wani mai suna Tujja Ali mai shekaru 18 da kuma Modu Bilal mai shekaru 19 , wadanda ake zargi da aikata laifin hada baki, barna da sace-sacen kadarorin gwamnati da suka hada da kusoshi 283 da wasu karafa.

Ya ce kayayyakin da aka sace ana zargin an samo su ne bayan tarwatsa wani turke na wutar lantarki da ke kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

Ya kara da cewa matasan na dauke da sanduna lokacin da suka aikata ta’asar.