✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama mutumin da ke kokarin yanka filin makabarta a Gombe

Mutumin dai ya ce wani dan siyasa ne ya sa shi, amma shi kuma ya musanta

Alummar unguwar Yerima da ke Karamar Hukumar Akko a Jihar Gombe sun cafke wani mutum mai suna Ibrahim Muhammad Danburam, yana yanka filin makabarta da nufin sayarwa.

Ibrahim Muhammad Inuwa, daya daga cikin al’ummar wannan unguwa da ya yi magana a madadin su yace ba su ji dadin yadda Danburam, ya zo yana kokarin sayar musu da filin makabartar tasu ba.

Ibrahim, ya ce babu shakka filin maigidan mutumin ne, wato Sanata Haruna Garba magayakin Gombe, wanda ya mallaka musu shi, amma yaron nasa ya zo yana kokarin sayarwa.

Sai dai ya ce mutumin ya zo yana yanka filin ne a kashin kansa don ya sayar ba tare da sanin wanda ya ba da shi ba.

Ya ce a lokacin da masu yanka filin suka fara shawagi a wajen don sanya alama, anga sun tono kashin wata gawa, amma ko a jikinsu, suka ci gaba da dora bulo a matsayin alama.

A cewarsa jama’ar unguwa ba su san an yanka filin ba sai gani suka yi ana haka, lamarin da ya sa suka yi magana, inda ya ce maigidansa ne ya sa shi wanda hakan tasa suka rike shi suka kira ’yan Jarida.

Yace da al’ummar unguwar suka tuntubi Sanata Haruna Garba kan ko shi ya aiko a yanka makabartar a sayar da wani yanki duk da cewa har yanzu ana binne mamata a ciki sai ya ce bai san da maganar ba kuma duk wanda suka kama zai yanka fili su hada shi da hukuma.

Ibrahim, ya ce Mai Unguwar su yana da masaniya a kan sayar da filin don bakinsu daya da Danburam din.

Da Aminiya ta tambayi Ibrahim Mohammad Danburam, mutumin da ake zargi da yanka filin, sai ya ce maigidan sa tsohon Sanatan Gombe ta arewa Haruna Garba ne ya ba da wajen wa kwamitin Da’awa kuma a lokacin da aka ba su sun shiga har inda ba filin da aka basu ba, shi yasa yanzu yake so ya cire ya bar iya na makabartar.

Da muka nemi jin ta bakin mai unguwar Malam Magaji, ya ki cewa komai domin hayaniya ta kaure inda ya nemi Danburam, ya gudu saboda jama’a sun fara neman dukan sa.

Wakilan unguwar nan take suka kira shugaban Da’awa na jihar Gombe Mohammad Lawan, dan jin ko yasan an basu wannan fili a tsawon shekarun da akayi sai yace shi bai da masaniyar an bai wa Kwamitin Da’awa fili har an gina makabarta.

Yanzu dai al’ummar unguwar ta Yerima quarters sun bayyana cewa duk wanda ya sake zuwa nan gaba da nufin yanka fili a wajen za su kamashi su hada shi da hukuma. Makabarta ta shekara fiye da goma ana binne mamata a cikin ta.