An kara kona ofishin ’yan sanda a Abiya | Aminiya

An kara kona ofishin ’yan sanda a Abiya

    Linus Effiong, Umuahia da Sagir Kano Saleh

’Yan bindiga sun sake cinna wa ofishin ’yan sanda wuta a safiyar Alhamis.

Maharan sun kona daukacin motocin da ke harabar tare da banka wuta a gine-ginen a ofishin ’yan sandan da ke Karamar Hukumar Bende ta Jihar Abiya

“Mun ji karar harbe-harbe, da muka fita waje sai muka iske ofishin ’yan sanda na ci da wuta,” inji wani makwabcin ofishin ’yan sandan da ke daura da Sakatariyar Karamar Hukumar.

Ya ce an kai harin ne bayan Gwamna Okezie Ikpeazu halarci liyafar tsohon Dan Majalisar Wakilai mai Wakiltar Bende, Hon. Nnenna Ukeje, a Sakatariyar.

An kai harin ne kasa da mako guda bayan ’yan bindiga sun kona ofishin ’yan sanda da ke Kasuwar Ubani a Karamar Hukumar.

Ana zagin haramtacciyar IPOB da kai hare-haren, amma ta sha musanta zargin.