✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kara dage wa’adin hade layin waya da lambar NIN

Mutum miliyan 75.3 sun yi rajista kuma za a rufe ranar 26 ga watan Yuli.

Gwamnatin Tarayya ta sake dage ranar rufe aikin hade layukan waya da lambar dan kasa ta NIN zuwa ranar 26 ga watan Yuli, 2021.

Ma’aikatar Sadarwar ta Kasa ce ta sanar da hakan tare da cewa zuwa yanzu mutum miliyan 75.3 sun hade lambarsu ta NIN da layukan wayansu, wadanda kowanne daga cikinsu ke amfani da layuka uku.

  1. Yadda ’yan ta’adda ke ribibin dibar ’yan bindiga a matsayin mambobinsu

Sanarwar da Daraktan Yada Labaranta, Ikechukwu Abinde, ya fitar ta ce, “An yanke shawarar ne saboda bukatar hakan da masu ruwa da tsaki suka gabatar, domin a dora a  kan nasarar da aka samu bayan bude karin cibiyoyin hada layukan waya da lambar NIN.

“Zuwa ranar 28 ga watan Yuni, 2021, muna da cibiyoyin yin rajista 5,410, wadanda tabbas za su kara saukaka hada layukan waya da lambar NIN.

“Idan ba a manta ba, a watan Disamba, 2020, cibiyoyi 800 kadai muke da su,” inji sanarwar.

Abinde tare da Shugaban Sashen Hulda da Jama’a na Hukumar Kula da Ba da Shaidar Dan Kasa (NIMC) sun ce karuwar cibiyoyin za ta ba wa ’yan Najeriya da mazauna kasar damar hada layukan wayoyinsu da lambarsu ta NIN.

A ranar 4 ga watan Mayu, 2021 ce Gwamnatin Tarayya ta kara wa’adin kammala aikin zuwa ranar 30 ga Yuni, domin saukaka wa jama’a samun yin hakan.

Gabanin nan, wa’adin farko da aka sanya ana kuma dagawa su shi ne 19 ga watan Janairu.

Daga baya aka mayar 9 ga Fabrairu, 6 ga watan Afrilu, sai kuma 6 ga watan Mayu.

Ministan Sadarwa, Isa Pantami ya yaba da yadda ’yan Najeriya suka rungumi hade layukan wayarsu da lambar NIN.

Shi ma Mataimakin Shugaban Hukumar Sadarwa ta Kasa, Farfesa Umar Dambatta tare da Darakta-Janar na Hukumar NIMC, Aliyu Azeez, sun yi kira ga jama’ar Najeriya da su tabbata sun hade lambobin wayoyinsu da lambar NIN.