✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An karrama dan agajin da ya tsinci miliyan 100

Dan agajin ya tsinci sama da Naira miliyan, amma ya mika su ga 'yan sanda domin nemo mai su.

An bai wa dan agajin Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Ikamatus Sunnah (JIBWIS), Salihu AbdulHadi Kankia, kyautar kujerar aikin hajji sakamakon dawo da Naira miliyan 100 da ya tsinta a Jihar Bauchi.

Wannan na zuwa ne lokacin bikin rufe taron shirin tafsirin watan Ramadan na bana da malaman addinin Musulunci suka yi a Jihar  Bauchi.

Daraktan Kungiyar Agaji na kasa, Injiniya Mustapha Imam Sitti ne, ya gabatar da Kankia don a yaba masa kan dawo da makudan kudin da ya yi.

A wani sako da JIBWIS reshen Jihar Bauchi ta wallafa a shafinta na Facebook ta ce, “Kankia ya gano wata jaka dauke da makudan kudade sama da naira miliyan 100.

“Maimakon ya tsere da kudin, sai ya garzaya ofishin ‘yan sanda inda ya mika jakar kudin, ‘yan sandan sun yi nasarar gano mai jakar, kuma sun tabbatar da babu abin da ya bata a ciki.”

Sanarwar ta kara da cewa, “Kungiyar Izala ta karrama shi da lambar yabo tare da biya masa kujerar aikin hajjin bana.

“Bugu da kari, dan majalisar dokokin Jihar Zamfara, Hon. Abdulmalik Zannan Bangud, ya ba shi kyautar Naira miliyan biyu.

“Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed na Jihar Bauchi, ya  ba shi kyautar mota kirar bas don fara neman kudi da ita.”