✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka kashe jagoran harin NDA da sace daliban Birnin Yauri

Sojoji sun kashe kasurgumin dan bindiga, Boderi, wanda ya kitsa harin da aka kai makarantar horas da sojoji ta NDA da Jami'ar Greenfield da ke…

Sojoji sun kashe kasurgumin dan bindiga, Boderi, wanda ya kitsa harin da aka kai makarantar horas da sojoji ta NDA da ke Kaduna. 

Boderi ne kuma ya kitsa hari da kuma sace dalibai a Jami’ar Greenfield da ke jihar, da kuma ’yan matan makarantar sakandaren Birnin Yauri da ke Jihar Kebbi, kamar yadda kakakin rundunar, Manjo-Janar Onyema Nwachukwu, ya sanar.

Sanarwar ta ce cewa a ranar Laraba aka kashe Boderi ne tare da wani shugaban ’yan bindiga mai suna Bodejo a kan hanyar Bada–Riyawa da ke kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.

“Majiyoyin leken asiri sun ba da rahoton cewa an kashe kasurgumin dan bindiga Boderi wanda ya kitsa sace daliban Birnin Yauri, Jami’ar Greenfield da kuma NDA, tare da wani mai suna Bodejo.

Ana ci gaba da kokarin tabbatar da hakan ta hanyar amfani da wasu hanyoyi,” in ji sanarwar.

A cewarsa, kun kwato babura 19 da ’yan ta’addan suka gudu suka bari da wasu abubuwa, kuma an kona su. 

a wani samame na daban da sojoji suka kai a yankin, ’yan ta’addan da suka yi amfani da shanu a matsayin garkuwa, sun bude musu wuta, amma suka mayar da martani cikin gaggawa.

“A yayin musayar wutar ta kusan awa daya, sojoji sun kashe biyu daga cikin yan ta’addan tare da kwato bindiga kirar AK 47 guda 1, da sauran abubuwa.

“Sai dai kuma an kashe wasu daga cikin dabbobin satan da da yan ta’addan ke amfani da su a matsayin garkuwa.

“Sojoji na ci gaba da bin diddigin yan ta’addan da suka tsere da kuma aikinsu na samar da tsaro a yankin.”