✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Murar tsuntsaye: An kashe kaji 27,000 a Bauchi

An dai sami rahoton barkewar cutar a Kananan Hukumomin Bauchi da Toro a jihar.

Gwamnatin jihar Bauchi ta ce ta kashe kaji kimanin 27,000 saboda takaita yaduwar cutar Murar Tsuntsaye da ta barke a jihar.

Shugaban Kwamitin Yaki da Yaduwar Cutar kuma Kwamishinan Aikin Gona da Raya Karkara na jihar, Alhaji Sama’ila Burga ne ya sanar da hakan yayin tattaunawarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ranar Juma’a.

An dai sami rahoton barkewar cutar a Kananan Hukumomin Bauchi da Toro a jihar.

Alhaji Sama’ila ya kuma ce gidajen gona guda biyu ne a Kananan Hukumomin da lamarin ya shafa kuma tuni suka kashe kaji 27,000 domin dakile yaduwar cutar a wasu sassa na jihar.

“Mun kashe kajin ne domin hana sauran kamuwa da ita.

“Gwamnatin jihar Bauchi ce ta kafa kwamitin a bangaren kokarin da take yi na dakile ci gaba da yaduwar cutar wacce yanzu haka ta bazu zuwa Kananan Hukumomi biyu,” inji shi.

Alhaji Sama’ila ya kuma ce an girke likitocin dabbobi 130 zuwa Kananan Hukumomin jihar 20 domin sa’ido a ko ina, kuma za su fara wayar da kan jama’a kan yadda za su gane cutar.

Ya kuma tunatar da masu gidajen gona da su tabbata suna bin dokokin da aka kafa domin kare kaji da sauran tsuntsaye daga kamuwa da cutar sau da kafa

Sai dai ya gargadi jama’a da su kiyayi cin kaji da tsuntsayen da suka kamu da cutar.