✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe kwamandan Taliban na Pakistan a Afghanistan

An kashe babban kwamandan a wani hari da aka kai a gefe hanya.

Abdul Wali Mohmand, wanda aka fi sani da Omar Khalid Khorasani, babban kwamandan Taliban na Pakistan ya mutu a wani harin a Afghanistan.

A ranar Litinin ne kungiyar Taliban ta Pakistan ta tabbatar da mutuwarsa, kuma ta ce nan ba da jimawa ba za ta fitar da wani karin bayani kan kisan.

An kai wa motarsa ​​harin bam ne a gefen hanya a lardin Paktika na kasar Afganistan da ke kan iyaka da Pakistan.

Kisan kwamandan na Taliban, wanda ya kai wasu munanan hare-hare a shekarun baya, na iya zama koma baya babba ga mayakan kungiyar.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta sanya Mohmand a cikin jerin sunayen mutanen da ake nema ruwa a jallo, kuma ta yi tayin bayar da tukuicin Dala miliyan uku domin samun bayanin inda yake.

Akalla kwamandoji biyu ne aka kashe a harin bam din na ranar Lahadi, mako guda bayan wani harin da jiragen yakin Amurka marasa matuki suka kai a birnin Kabul, wanda ya yia kashe shugaban al-Qaeda Ayman al-Zawahiri.

Ana ganin Abdul yana da kusanci da jagoran al-Qaeda, Osama bin Laden da kuma Ayman al-Zawahiri, sai dai ba a san ko akwai wata alaka tsakanin harin da jirgi mara matuki ya kai da tashin bam ba.

Kungiyarsa ta kai wasu munanan hare-hare a Pakistan, ciki har da wani wanda aka kai a Gabashin birnin Lahore a shekarar 2016.

An dai yi zaman sasantawa tsakanin gwamnatin Pakistan da kungiyar tsawon watanni biyu da suka gabata yayin da ake gudanar da tattaunawar zaman lafiya da kungiyar Haqqani ta Taliban ta Afganistan.

TTP ta kashe ’yan Pakistan kusan 80,000 a cikin kusan shekaru 20 da tashe-tashen hankula.