✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe mai tsaron lafiyar alkali an sace ta

Maharan sun sace alkalin da direbanta sannan suka kashe dan sandan da ke ba ta kariya.

Wasu mahara sun kashe dan sandan da ke tsaron lafiyar wata babbar alkali sannan suka yi awon gaba da ita da direban ta zuwa inda ba a sani ba. 

’Yan sanda sun tabbatar da sace Mai shari’a Joy Uwana da direbanta bayan an kashe dan sandan a kan hanyar Uyo-Okobo, Karamar Hukumar Oron ta jihar Akwai Ibom.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito kakakin ’yan sanda jihar, SP Odiko Macdon, yana cewa rundunar ta fara bincike don bin diddigin wadanda suka aikata laifin da kuma kwato alkalin da direbanta lafiya.

SP Odiko Macdon, ya ce “Kwamishinan ’yan sanda, Olatoye Durusinmi ya ba da umarnin yin cikakken bincike kan lamarin.

“Muna bincike don tabbatar da cewa an yi abin da ya dace.

“Zuciyarmu na cike da bakin ciki musamman ga iyalin dan sandan da aka yi wa kisan gilla.

“Wannan abun takaici ne,”in ji Macdon.

Ya bukaci jama’a a jihar da su ci gaba da al’amuransu yadda suka saba yayin da rundunar ke gudanar da bincike.

Macdon ya ce rundunar za ta ci gaba da yin aiki tare da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Ya kuma gargadi masu aikata laifuka a jihar cewar rundunar ba za ta saurara musu ba.