✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe malamin addinin Musulunci Sheikh Goni Aisami a Yobe

Kisan fitaccen malamin ya jefa al’umma cikin rudani yayin da dama suka shiga alhini.

An kashe wani fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Goni Aisami Gashuwa a Jihar Yobe.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, ana zargin wasu ’yan bindiga da aikata wannan danyen aiki da misalin karfe 10 na daren ranar Juma’ar da gabata.

Bayanai sun ce an kashe malamin ne a kan hanyarsa ta zuwa garin Gashuwa daga Jihar Kano.

Wata majiyar jami’an tsaro a garin Jaji-Maji da ke zaman shalkwatar Karamar Hukumar Karasuwa, ta shaida wa Aminiya cewa, maharan sun biyo shi ne a motar Sharon, inda suka tare motarsa bayan ya fita daga kauyen Chakama mai tazarar kilomita 3 zuwa garin Jaji-Maji.

Majiyar ta ci gaba da cewa, “marigayi Aisami shi kadai ne a motar kuma da alama sun biyo shi ne bisa zaton yana dauke da kudi, a kan hanyarsa daga Kano zuwa garinsu na Gashuwa.”

Majiyar ta kara da cewa, “bayan sun harbe shi a ciki tare da soka masa wuka a jiki, sannan suka ja gawarsa zuwa gefen hanya cikin surkuku kuma cikin ikon Allah ba su samu damar barin wurin ba har wayewar gari.

“A cewar mazauna garin na Jaji-Maji, ana haka sai ga jama’a masu tafiya gona, wanda nan take suka shaida wa Lawanin Jaji-maji, Lawan Manaja halin da ake ciki.

“Nan da nan Lawanin ya kai rahoton ga ’yan sanda da ke aiki a garin nan Jaji-Maji.

“Ana zargin wasu mutane biyu da kisan malamin, wanda tuni ’yan sanda sun kama su.

“An mika ababen zargin tare da gawar malaman zuwa Damaturu, babban birnin Jihar Yobe don ci gaba da bincike.”

Kisan malamin ya tayar da hankula a garin Gashuwa da Jihar Yobe baki daya, kasancewarsa mutum mai kokari kuma malami mai karantar da al’umma sama da shekaru 30 kamar yadda mutanen na Gashuwa suka bayyana wa Aminiya.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Yobe, ASP Dungus Abdulkarim ya tabbatar da faruwar lamarin.

ASP Dungus ya shaida wa Aminiya cewa, wadanda ake zargi da aikata laifin yanzu haka suna hannun jami’an tsaron binciken manyan laifuka (CID) a Damaturu.

Ya ce za a sanar da manema labarai halin da ake ciki a yayin da bincike tuni ya kankama.

Sai dai BBC ya ruwaito kakakin ’yan sandan yana zargin wasu sojoji ne suka kashe malamin.

ASP Dungus ya ce sojojin biyu da suka yi kokarin sace motar malamin bayan harbe shi an damkesu.

Gwamna Mai Mala Buni a wata sanarwa da ya fitar a Damaturu, ya ce wannan kisa abin takaici ne da alla-wadai, don haka za a binciki lamarin.